16 Afirilu 2020 - 04:59
​Guterres Ya Mayar Wa Trump Da Martani Kan Yanke Tallafin Amurka Ga WHO

Babban sakataren majalisar dinkin duniya Antonio Guterres ya mayar wa shugaban Amurka Donald Trump da martani kan matakin da ya dauka na yanke tallafin Amurka ga hukumar lafiya ta duniya (WHO).

(ABNA24.com) Babban sakataren majalisar dinkin duniya Antonio Guterres ya mayar wa shugaban Amurka Donald Trump da martani kan matakin da ya dauka na yanke tallafin Amurka ga hukumar lafiya ta duniya (WHO).

Kamfanin dillancin labaran AFP ya bayar da rahoton cewa, a cikin wani bayaninsa a daren jiya Talata, Babban sakataren majalisar dinkin duniya Antonio Guterres, bayyana cewa yanzu ba lokaci ne da wani ko wata kasa za su ce sun yanke tallafin da suke baiwa hukumar lafiya ta duniya ba.

Ya ce yanzu lokaci na hada kai tsakanin dukkanin al’ummomin duniya domin tunkarar annobar da take yin barazana a gare su, tare da ajiye duk wasu batutuwa na siyasa a gefe guda.

A jiya ne Trump ya sanar da cewa Amurka ta yanke dukkanin tallafin da take baiwa hukumar lafiya ta duniya, saboda abin day a kira gazawar hukumar wajen tunkarar annobar corona, wadda ta cutar da Amurka fiye da kowace kasa ta duniya a halin yanzu.


/129